“Batun sakin Nnamdi Kanu baya cikin tattaunawa ta da gwamnonin Kudu maso Gabas” – Obasanjo

Olusegun, Obasanjo, Batun, sakin, Nnamdi Kanu, gwamnonin, Kudu maso Gabas
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa batun sakin Nnamdi Kanu baya cikin tattaunawarsa da gwamnonin Kudu maso Gabas a jihar Enugu ranar...

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa batun sakin Nnamdi Kanu baya cikin tattaunawarsa da gwamnonin Kudu maso Gabas a jihar Enugu ranar Talata.

Tsohon shugaban kasa kuma tsohon sakataren kungiyar Commonwealth, Emeka Anyaoku ya gana da gwamnonin bisa gayyatar da suka yi da kansu inda suka tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban yankin da shirin gwamnatin tarayya na sakin Kanu da aka ce ba ya cikinsa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya fitar ranar Laraba.

Karin labari: Kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya sun sanar da sake duba kudin wuta

Ya bayyana cewa, batutuwan da aka tattauna a taron sun hada da ci gaban yankin, tsaro da samar da ababen more rayuwa.

Sauran sun kasance tattalin arziƙi da haɗin gwiwa wanda ke nufin dacewa da ajandar ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

“Ganawar da su ta kasance bisa gayyata ta da kuma na Cif Emeka Anyaoku kafin a fara taron nasu. Batun Nnamdi Kanu ba ya cikin ajanda kuma ba a tattauna a gabana ba,” inji Obasanjo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here