‘Yan sanda sun tabbatar da harin da ‘yan bindiga suka kai a Masallacin Kaduna, inda suka kashe masu ibada 7

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna a ranar Asabar din da ta gabata ta tabbatar da kashe mutane 7 a lokacin da suke gudanar da sallah a wani masallaci da ke kauyen Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara a jihar.

Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.

Hassan yace “da misalin karfe 8:00 na dare. a ranar Juma’a, mun samu labari daga kauyen Saya-Saya cewa, an kashe mutane shida a lokacin da suke gudanar da sallar  (Isha’i) a wani Masallaci.

“’Yan bindiga kimanin tara ne a kan babura suka zo suka far wa mutanen da ke cikin Masallacin. “A wajen, sun harbe mutum shida a lokacin da suke sallah a wani masallaci a kauyen.

Hassan ya ce, ‘yan bindigar sun kuma koma wani masallaci da ke Tashar Dauda, ​​wanda shi ma a karamar hukumar Ikara, suka kashe mutum daya, uku kuma suka samu raunuka.

Ya ce barayin sun tafi da babura hudu. “Samun bayanan, DPO Ikara ya tattara jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru. Ya ce saboda kusanci ne ‘yan fashin suka tsere zuwa daji kafin isowar jami’an tsaro.

“Kawo yanzu ba a kama wani mutum a wurin da lamarin ya faru ba amma an kwato harsashi guda biyar na bindigar AK49.”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here