
Gwamnatin Taraba ta dauki matakan haramta hawan babur kowane iri a fadin Jalingo babban birnin jihar, da kuma takaita zirga-zirgar Babura masu kafa uku da aka kira da Keke Napep tsakanin karfe 6 na safe zuwa karfe 8 na daren kowace rana.
Cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin jihar ta Taraba ta ce dole ne ta sanya daukar matakan domin dakile karuwar aikata miyagun laifuka a sassan birnin Jalingo.
Karanta wannan: Yanzu-yanzu: Gwamnan Jihar Filato Mutfwang ya ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 24
Mahukuntan sun kara da cewar dukkanin wanda aka samu da laifin karya dokokin zai gurfana gaban kotun tafi da gidanka da aka kafa, haka zalika za kuma a kwace ababen hawan da aka kama.
Matsalar tsaro dai ba sabon abu bane a jihohin arewacin Najeriya da dama, kama daga arewa maso yamma inda ake fama da ta’addancin masu sata da garkuwa da mutane, zuwa yankin arewa maso gabas da suka yi fama da mayakan Boko Haram.
Karanta wannan: Amurka da Burtaniya sun kara kai hari kan mayakan Houthi
A jihar Adamawa da ke mawaftaka da Taraba dai har yanzu dokar hana hawa babura bata daina aiki ba a fadin jihar, yau dai tsawon shekaru akalla 10, kamar yadda a lokutan baya mahukuntan jihar suka sha nanatawa.