Amurka da Burtaniya sun kara kai hari kan mayakan Houthi

Joe Biden 2
Joe Biden 2

Amurka da Birtaniya sun sake kai wasu jerin hare-hare na hadin gwiwa kan mayakan Houthi a Yemen.

Kasashen biyu sun ce sun kai hare-haren ne a kan wuraren ayyukan soji, a matsayin martani ga hare-haren da ‘yan Houthin masu samun goyon bayan Iran ke kai wa a kan jiragen ruwa na kauwanci a tekun Maliya.

Wannan shi ne hari na biyu na hadin gwiwa da Amurka da Birtaniya suka tsara tare da kuma kaiwa a kan wuraren ‘yan Houthi a kasar ta Yemen.

Harin ya kasance mafi girma a kan na farko, da nufin kara kassara karfin ‘yan Houthin na kai hare-hare.

Karanta wannan: Sakataren harkokin wajen Amurka zai kawo ziyara Najeriya

Jiragen sama na yaki da dama ne da suka tashi daga kan wani katafaren jirgin ruwa na dakon jiragen yakin suka kai harin a tsakiyar dare.

Ma’aikatar tsaro ta Amurka Pentagon ta ce an yi nasarar kai harin a wurare takwas na ‘yan Houthi, ciki har da wata ma’ajiyar makamai ta karkashin kasa, da wuraren da ke da alaka da makamai masu linzami da kayayyakin leken asiri ta sama da na kai hari na mayakan.

Rahotanni daga Yemen na cewa an ji manya-manyan fashewa a babban birnin kasar, Sanaa, wanda ke hannun ‘yan Houthin, da ke samun goyon bayan Iran.

Wannan dai shi ne mataki na baya-bayan nan a kan mayakan na Houthi, da ke kai hari a kan jiragen ruwan kasuwanci a tekun Maliya, harin da suke cewa suna kai wa ne a matsayin martanin yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da Hamas.

Karanta wannan: Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da matakin Twitter

Shugaban Amurka Joe Biden da Firaministan Birtaniya Rishi Sunak sun tattauna kan batun ta waya.

Fadar gwamnatin Amurka, White House, ta ce shugabannin biyu sun jaddada kudurinsu na tabbatar da abin da suka kira ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma kare masu safarar ruwan daga duk wasu hare-hare.

A wata sanarwa ta daban da Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta fitar dangane da harin ta ce, jiragen sama na yaki kirar RAF Typhoon guda 4 wadanda suka tashi daga Cyprus sun yi ruwan bama-bamai a sansanonin soji biyu da ke kusa da wani filin jirgin saman soji a Yemen din.

Sakataren tsaro na Birtaniyar GrantShapps ya bayyana harin a matsayin na kare kai daga hare-haren ‘yan Houthi da ba za a lamunta ba a kan jiragen ruwa na kasuwanci.

Kwana goma sha daya da ya gabata Amurka da Birtaniya suka kai hari na farko irin wannan ta sama da ya kai gommai a kan wurare na soji da suka hada da jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami da wuraren na’urorin tsinkayen jiragen sama, wadanda suka ce ‘yan Houthin na amfani da su wajen kai hare-haren a Maliya.

Karanta wannan: Gwamnatin Kogi ta haramta bada lasisi ga masu hako Ma’adanai a Jihar

A wancan lokacin an sa ran harin zai sa ‘yan Houthin su daina abin da suke yi, to amma ko alama sai ma suka ci gaba, da kai farmakin kan jiragen ruwa na kasuwanci suka lalata da dama.

A ‘yan makonnin da suka gabata Amurka ita kadai ta rika kai karin hare-hare a kan mayakan na Houthi inda ta ce tana kai wa ne kan makamai masu linzami na mayakan a daidai lokacin da ake shirin harba su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here