Majalisar dattawa, a ranar Laraba, za ta yi muhawara kan hukuncin wata babbar kotun tarayya da ke zama a Umuahia, Abia, wadda ta soke sashe na 84 (12) na dokar zabe mai cike da cece-kuce.
Hakan ya biyo bayan wani batu da Sanata George Sekibo (PDP-Rivers) ya gabatar yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Sashin ya bukaci ministoci, shugabannin hukumomin gwamnati da sauran masu rike da mukaman siyasa da su yi murabus kafin su shiga zaben fidda gwani, ko babban taro jam’iyya da sauran ayyukan zabe.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa a ranar 18 ga watan Maris ne kotun ta soke sashe na 84(12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima, inda ta ce hakan ya saba wa tanadin kundin tsarin mulkin kasar.
Kotun, a cikin hukuncin da mai shari’a Evelyn Anyadike, ta yanke, ta ce sashin “ya sabawa kundin tsarin mulki ba, kuma baya cikin ka’ida, ba shi da amfani kuma ba shi da wani tasiri”.
Sekibo, yayin da yake akan odar majalisar dattijai ta 10 da 11 wadda ta bayar da dama kan yin Magana akan dokar zabe wadda ta fito daga majalisar tarayya, don haka ya kamata a hada majalisar a matsayin jam’iyya a cikin karar.
Don haka ya bukaci a tattauna batun a zaman majalisar a yau (Talata) domin kaucewa sanya gaba a kan dokokin da majalisar tarayya ta kafa.
Sanata Chukwuka Utazi (PDP-Enugu) ya goyi bayan kudirin.
Sai dai mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya bayar da shawarar dage muhawara kan batun zuwa ranar Laraba tunda shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da sauran ‘yan majalisar da dama ba su halarci taron ba.
NAN ta ruwaito cewa sashin yana cewa: “Babu wani dan siyasa a kowane mataki da zai zama wakilai ko kuma a zabe shi a babban taron ko taron kowace jam’iyyar siyasa don gabatar da ‘yan takara a kowane zabe”.










































