Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, ya ce karancin iskar gas ne ya janyo matsalar wutar lantarki a kasar.
Abubakar ya bayyanawa manema labarai na fadar gwamnatin tarayya hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Laraba a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ministan ya ce ana kokarin ganin an shawo kan lamarin, inda ya kara da cewa Najeriya na da karfin megawatt 8,000 a ajiye.
“Batun da muke fuskanta a halin yanzu ba wai kawai sakamakon karancin ruwan da aka samu ba ne, wanda mafi yawanku kuka kama a cikin rahoton ku; wannan yana daga cikinsa; amma ba yawa daga wannan kusurwar.
“Abin da ya sa muke fuskantar lamarin a yanzu shi ne sakamakon karancin iskar gas da kuma wasu na’urorin samar da wutar lantarki da ake aikin gyarawa.
“Yanzu haka NNPC ta yi maganin matsalar ta Gas kamar yadda kuke gani a ko’ina, da man jiragen sama, da man fetur duk sun samu a fadin kasar nan.
“Injinan Janareto ba sa iya samar da wuta saboda rashin iskar gas; To, Na san wasunku suna sane; kwanaki biyu kacal da suka wuce, na kira taron gaggawa wanda ba a taba ganin irinsa ba’’ in ji Ministan.
Ya ce a karon farko ya kawo dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da NNPC da Agip da Shell zuwa hukumar NERC da GENCOS kamar kamfanin wutar lantarki na Neja-Delta da TCN da ma’aikatar.
Abubakar ya ce taron wanda ya hada da mai baiwa shugaban kasa shawara kan samar da ababen more rayuwa, an shafe tsawon yini ana kokarin samar da mafita.
Abubakar ya ce, an kafa kwamitoci domin su tanadi yadda za a samu karin megawatts domin a ka’ida, matsalar ta shafi iskar gas ne.
A cewarsa, akwai bukatar samun kwangilar iskar gas tsakanin kamfanonin da ke samar da iskar gas – wasu kwangiloli ne, wasu kuma ba.