Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Bliken zai kai ziyara Cafe Verde da Cote d’Ivoire da nan Najeriya da kuma Angola daga ranar 21 zuwa 26 ga watan Janairun 2024.
A yayin ziyarar, sakataren zai yi tsokaci kan yadda Amurka ta kara inganta hadin gwiwa tsakaninta da Afirka tun bayan taron shugabannin Amurka da Afirka, wanda ya mayar da hankali kan sauyin yanayi da abinci, da kuma kiwon lafiya.
Karanta wannan: Majalisar Wakilan Amurka za ta fara shirin tsige shugaba Joe Biden
Haka kuma, zai jaddada yadda dangantakarsu ta fuskar tattalin arziki da kasashen da yake ziyara za ta mayar da hankali nan gaba, da yadda Amurka ke zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa a nahiyar Afirka, domin bunkasa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi a gida da ma nahiyar, da kuma karfafa Afirka a duniya.
Karanta wannan: Gwamnatin Kano za ta kashewa makarantun firamare 3 Naira Biliyan 8
Kazalika, Sakataren zai bayyana kokarin hadin gwiwa da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) don tinkarar kalubalen yankin da kuma goyon bayan shugabannin Afirka wajen warware rikice-rikice, musamman a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Wannan ziyarar na nuni da yunkurin da Amurka ke yi na ci gaba da yin cudanya da Afirka.