Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya jagoranci shugabannin jam’iyyar na Kano zuwa wata ganawar sirri da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar Villa dake Abuja.
Daga cikin tawagar akwai mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin da karamar ministar babban birnin tarayya Dakra Mariya Bunkure, da Nasiru Gawuna da mataimakinsa, Murtala Sule Garo da Abdullahi Abbas da dai sauransu.
Karanta wannan: Hukumar NAFDAC ta kama kwalin dunkulen Maggi na Naira Miliyan 4.5 a Jihar Sokoto
Taron na ranar Alhamis ya zo ne mako guda bayan da kotun koli ta yanke hukuncin tabbatarwa da babban abokin hamayyar Gawuna, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin zababben gwamnan jihar.
A watan Maris din da ya gabata ne dai mulkin jihar ya bar jam’iyyar APC bayan zaben da Gawuna ya samu kuri’u dubu 890 da 705 yayin da shi kuma Abba Kabir ya samu kuri’u miliyan 1 da dubu 19 da 602, wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.
Karanta wannan: Barkewar annobar Kwalara a Zambiya ta kashe Mutane sama da 400
Bayan turka-turkar aka yi daga kotun korafe-korafen zabe da daukaka kara, a ranar 12 ga watan Janairu ne kotun koli ta tabbatar da Abba Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano, inda ta soke hukuncin kotun daukaka kara da ta bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ba a bayyana ajandar taron na ranar Alhamis ba, kuma wadanda suka halarci taron ba su yi magana da manema labarai na fadar shugaban kasar ba.