Jami’ar Bayero ta Kano ta dauki dalibai kusan 200 a fannin likitanci daga Sudan, sakamakon yakin da ake yi a kasar.
Shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Kano yayin bikin ranar gidauniyar kwalejin kimiyya da aikin jiya karo na hudu.
Karanta wannan: JAMB ta amince da yin rijista kyauta ga masu bukata ta musamman
Farfesa Abbas ya ce jami’ar ta kafa sabuwar cibiyar bincike da zata mayar da hankali kan binciken lafiya da horar da sana’o’i.
Ya ce cibiyar za ta bada gudummawa ga ci gaban fannin kiwon lafiya.
Karanta wannan: Jami’ar Bayero ta horas da Matasa domin zama Shugabanni Nagari
Da take jawabin maraba, shugabar kwalejin kimiyyar lafiya ta jami’ar, Farfesa Aisha Kuliya Gwarzo, ta nuna godiya ga duk wanda ya bada gudunmawa a gidauniyar, da suka hada da dalibai da ma’aikata, da masu hannu da shuni, musamman ma jami’an gudanarwar jami’o’in da suke ba da gudunmawa a karkashin jagorancin shugaban jami’ar Bayero.