Jami’ar Bayero ta horas da Matasa domin zama Shugabanni Nagari

BUK 4 300x145 1
BUK 4 300x145 1

Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas ya bayyana ilimi don ci gaba mai dorewa a matsayin abin da zai inganta rayuwar matasa.

Farfesa Abbas ya bayyana haka ne yayin taron da cibiyar nazarin jinsi ta jami’ar Bayero ta shiryawa matasa karo na 6.

Taron da ta cibiyar ta shirya shi akan hanyoyin samar da ilimi don ci gaba mai dorewa.

Karanta wannan: Daliban jami’ar FUDMA da aka yi garkuwa da su sun shaki iskar yanci

Shugaban jami’ar ya ce cibiyar ta samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa don ci gaba.

Jami'ar, Bayero
BUK Senate 1

Acewarsa ire-iren wadannan taruka zasu karfafawa matasa Gwiwa da nufin samar da ci gaba mai dorewa.

Da take jawabi shugabar cibiyar, Dakta Suwaiba Sa’id Ahmed ta ce cibiyar tana horas da matasa domin zama nagartattun shugabanni da za su kawo ci gaba mai dorewa a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here