Shugaban Kasa Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin mai rikon amana, gaskiya da adalci da kuma kishin kasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne cikin sakon taya murnar karin shekara ga tsohon shugaban kasar da ya cika shekara 81 a duniya.
Ya yaba da kwarewar shugabanci da samun nasarori na tsohon shugaban kasar, a lokuta mabanbanta a matsayin shugaba.

Karanta wannan: Daliban jami’ar FUDMA da aka yi garkuwa da su sun shaki iskar yanci
Ya kuma yaba wa Buhari kan tarin ayyukan raya kasa da ya gudanar a bangarori da dama zamanin mulkinsa.
Tinubu ya kwatanta tsohon shugaban kasar a matsayin kyakkyawan misali na mutumin kirki, da biyayya da nuna kauna, da kishin kasa, da rikon amana a tafarkin ci gaban kasa.