Malaman makarantun firamare da ke babban birnin tarayya Abuja, sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani a wannan Larabar, kan wasu basussukan da su ke bin wasu kananan hukumomi a yankin.
Shugaban kungiyar malamai ta Najeriya reshen Kubwa, Kwamared Ameh Baba, ya tabbatar da yajin aikin da malaman suka fara a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa mambobinsu suna bin majalisun yankin bashin albashi da karin girma, da kuma mafi karancin albashi daga shekarar 2011.
Shugaban kungiyar ta NUT ya ce wani bangare na yarjejeniyar da suka yi na janye yajin aikin da suka yi a baya a watan Nuwamban da ya gabata ya samo asali ne saboda tsoma bakin Sanatan babban birnin tarayya, Philip Aduda, wanda ya ce za su fara aiwatar da bukatun nan take.
“Amma har yanzu ba su cika alkawarin ba, kuma ga dukkan alamu sun fi damuwa da taron yakin neman zabensu wanda a halin yanzu ke mamaye fadar,” in ji shi.
Daily Trust ta ruwaito cewa malaman firamare sun shiga yajin aikin kusan sau uku a bara. Yajin aikin na karshe da suka fara ya dauki tsawon makonni biyu ana yi.











































