Wata Kungiya mai zaman kanta da ke fafutukar kawo sauyi ga tsarin Ilimi na Almajiri, KDC Foundation, ta gudanar da taron wayar da kai ga malaman Makarantun Tsangaya, domin tattaunawa kan samar da sabuwar manhaja da za ta tsara tafiyar da makarantun Tsangaya.
Tattaunawar wadda ta gudana a ranar Litinin, a Kano, ta samu halartar masu ruwa da tsaki daga gwamnatin tarayya da na jiha, malaman makarantu, da kafafen yada labarai, inda aka tattauna kan hanyoyin zaburar da malaman Islamiyya domin su amince da sauye-sauye masu kyau daga manhajar karatu.
Shugaban gidauniyar, Khalifa Muhammad Dankadai, ya ce makasudin taron shi ne domin jin ta bakin malaman Islamiyya kan yadda suke kallon manhajar da kuma samun abubuwan da suka dace don tsara yadda ya dace da ra’ayinsu.
Ya ce “ta hanyar nazarin abubuwan da malaman Islamiyya suka bayar, an tabbatar da cewa sun amince da tsarin kuma a shirye suke su yi aiki da shi a duk lokacin da aka samu wanda shi ne babban damuwarmu. Domin dole ne su yarda kuma su yi aiki tare da tsarin karatun sannan za mu cimma burinmu na gyara tsarin.
“Don haka za mu yi la’akari da ra’ayoyinsu tare da ba su ‘yanci don gudanar da tsarin da kansu. Daga cikin abin da za mu yi shi ne koyar da Turanci da Lissafi, da kuma koyar da yara kanana sana’o’in kasuwanci ta yadda za su daina barace-barace a kan tituna da kuma yin ado da kyau kamar sauran daliban,” inji shi.
Ya ce sun dauki nauyin duk masu ruwa da tsaki ciki har da gwamnatin jihar a fadin Makarantun Tsangaya guda 10 a kowace Jihohi 6 da aka zaba a Arewa.
Wani malami a tsangayar ilimi ta Jami’ar Bayero Kano (BUK), Dokta Kamilu Ibrahim ya ce alamu na nuna cewa a wannan karon kokarin sake fasalin Makarantun Tsangaya zai yi nasara duba da tsarin da aka kafa.
“Wannan ya sha bamban da sauran yunƙurin da suka yi a baya domin wannan ya sa su kansu Malaman Makarantun Tsangaya su taka nasu rawar kuma na tabbata idan aka yi tafiya mai kyau nasara tana kan su.”
Shima da yake magana a madadin Malaman Makarantun Tsangaya, Malam Jazuli ya ce sun jima suna jiran wannan shiri, kasancewar a baya an yi da yawa, amma babu wanda ya samu nasara a cikinsu, ya kara da cewa wannan shi ne karo na farko da aka yi alkawarin shigar da su cikin dukkan ayyukan da za’a yin a fito da sabon tsarin.
Ya ce Malaman Makarantun Tsangaya a shirye suke su karbe su kuma su yi aiki da tsarin karatun da Gidauniyar ta yi alkawarin zayyana nan ba da jimawa ba.