Shugaban Kwamitin riko na Jam’iyyar APC Mai Mala Buni da Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar a ranar Talata sun jagoranci zaman sulhu kan rikicin jam’iyyar APC na jihar Kano.
Solacebase ta ruwaito cewa akwai bangarorin guda biyu a APC t jihar Kano. Bangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta wanda suka zabi Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaba, da bangaren da Gwamna Abdullahi Ganduje Ke jagoranta, wanda suka zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba.
Sai dai wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Hamza Muazu a watan Disambar da ya gabata, ta amince da zaben mazabu da na kananan hukumomi da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya gudanar.
Da rashin gamsuwa da hukuncin kotun, bangaren Abdullahi Ganduje ya garzaya kotun daukaka kara.
A zaman karshe na Kotun daukaka kara a ranar 21 ga watan Janairu, 2022, kotu ta ce zata sanar da lokacin yanke hukunci.
A ranar Talata ne aka gudanar da zaman sulhu tsakanin bangarorin Ganduje da Shekarau a jihar Kano a Abuja. I
Wadanda suka halarci zaman sulhun sun hada da Sanata Ibrahim Shekarau, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, dan majalisar wakilai mai wakiltar Kamar Hukumar birnin Kano Shaaban Ibrahim Sharada, Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa da sauran su.
A cewar Gwamna Mohammed Badaru, bangarorin biyu sun nuna shirin yin sulhu da aiki tare da mutunta juna.













































