Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta nada Sanata Kashim Shettima, tsohon gwamnan Borno a matsayin shugaban kwamitin amintattu na kwalejin Future Assured da ke Maiduguri.
Gidauniyar Aisha Buhari Foundation ce ta gina kwalejin a Maiduguri domin daukar nauyin karatun wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a jihar.
Da take kaddamar da kwamitin gudanarwa na kwalejin mai mutum 11 da Shettima ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Talata, Aisha Buhari ta bukaci mambobin su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu da sadaukarwa.
Ta ce “An zabe a matsayin mambobin hukumar makarantar domin kula da harkokin gudanarwar kwalejin. Aiki ne mai girma, amma na yi imani yana da wuyar gaske.
“Saboda haka, ina addu’a cewa mu hada kai don cimma burinmu na bawa ‘ya’yanmu ilimi mai amfani, mu tabbatar da makomarsu da kuma bunkasa al’umma ta hanyar yi wa al’umma hidima.”
Ta bayyana godiya ga gwamnati da al’ummar Borno bisa goyon baya da hadin kai.
Aisha Buhari ta kuma godewa gidauniyar TY Danjuma da sauran abokan cigaban da suka bada goyon baya domin samun nasarar aikin.
A jawabinsa na karbar aikin, Shettima ya bayyana godiyarsa ga uwargidan shugaban kasar da ta yi masa wannan nadin.
Ya bayyana kudurinsa na ganin an aiwatar da aikin ta hanyar tabbatar da cewa an kiyaye ka’idojin makarantar domin amfanin marayu.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa wasu da aka nada a hukumar sun hada da Mrs Halima Buhari Sherrif a matsayin sakatariya, Dakta Muhammad Idris, Hadi Uba, Muhammad Albishir, Farfesa Bulama Kagu, Farfesa Aisha Ahmed, Hon. Asabe Vilita-Bashir, Dr Hajo Sani, Nana Liberty da Hauwa Ngoma.