2023: NLC ta Caccaki Gwamnonin Arewa da na Kudanci

NLC New new
NLC New new

Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta caccaki gwamnonin Arewa da na Kudanci kan muhawarar da suke yi na yankin da za a mika wa mulki a 2023.

Kungiyar kwadago ta NLC ta ce abin mamaki ne yadda gwamnoni ke yin cacar baki akan batun.

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC Ayuba Wabba ya fada hakan ne a Abuja a ranar Laraba cewa kalaman gwamnonin na baya-bayan nan sun nuna rashin kulawa da wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki.

Wabba ya ce bai dace a yi amfani da zabukan 2023 a matsayin uzuri don bayyana da “sabbin matsalolin rikice -rikicen tsaro a Najeriya ba.”

Ya yi magana ne a wani taron tattaunawa kan inganta rayuwar yan Najeriya,’ wanda NLC ta shirya.

Idan za a iya tunawa, Kungiyar Gwamnonin Kudancin ta yi taro a Legas a ranar 5 ga Yuli kuma ta nemi yankin ta ya samar da shugaban kasar a 2023.

Haka kuma a ranar 27 ga watan Satumba, Kungiyar Gwamnonin Arewa ta gana a Kaduna inda suka bayyana shugabancin karba -karba a matsayin abin da ya sabawa kundin tsarin mulki.

Sai dai Wabba ya ce: “Lallai abin takaici ne kuma abin damuwa yadda‘ yan siyasar mu ke samun lokaci da tada jijiyar wuya a kan 2023 lokacin da 2021 ke cike da gaggarumar matsalar rashin tsaro, tashin hankali da bacin rai, da cunkuga tarin sansanonin gudun hijira wato IDP.

A cewar bayanin “Muna nuna bakin cikin mu da irin wadannan kalaman na nuna rashin kulawa da mummunan halin da wahalhalun da talakawan Najeriya da ma’aikatan ta ke fama da shi da tabarbarewar harkokin mulki a kasarmu.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here