Dan-majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Mazabar Oron a majalisar tarayya, Nse Ekpenyong, ya mutu.
An rawaito Mista Ekpenyong, mai shekaru 58, ya mutu ne a ranar Asabar.
Shugaban Karamar hukumar Mbo a jihar Akwa-Ibom, Asuqwo Eyo, shi ne ya tabbatar da mutuwarsa a ranar Litinin.
Yace kafin rasuwar Mista Ekpenyong bai kwanta rashin Lafiya ba.
Shi dai Mistw Ekpenyong kafin rasuwarsa yana wakilitar mazabar Oron a Majalisar Tarayya daga jihar Akwa-lbom ne, kuma zai kammala wa’adin Zango na biyu ne a Majalisar cikin watan Mayun shekarar 2023.
Kazalika tsohon Mamba ne a majalisar dokokin jihar Akwa Ibom, kuma tsohon mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar.
Kafin shigarsa harkokin siyasa ya yi aiki matsayin Manajan Darakta a kamfanin Based/Investment Trust Co Nigeria Ltd daga baya kuma ya zama mamallakin kamfanin Brule Integrated Nigeria Ltd.