Jam’iyyar PRP ta gargadi jama’a game da wani jadawalin kudaden sayan takardun tsayawa takara da ake yadawa cewa na jam’iyyar ne, inda ta kwatanta hakan a matsayin yaudara.
A cikin wata sanarwa da shugaban Jam’iyyar na Kasa Mista Falalu Bello, ya fitar ranar Litinin a Abuja, yace kudaden takardun tsayawa takarar da ake zargin sun kai Naira 500,000 da kuma Naira 200,000 na mukaman shugaban kasa da na gwamna.
“Sai kuma Naira 100,000 da Naira 80,000 na mukaman Yan Majalisun Dattawa da na Wakilai; sai kuma Naira 70,000 na kujerun Yan Majalisar Dokokin Jihohi”.
Yace: “Hankalin Jam’iyyar PRP ya kai kan takardar jadawalin kudaden sayan takardun takarar na bogi da wasu bata gari dake son damfarar al’umma suke yadawa.
“Saboda haka wannan Jadawalin bogin dake zagayawa cikin al’umma ya kamata su yi fatali da shi domin ba daga Jam’iyyar PRP ya fita ba.
Bello ya bayyana cewa bisa biyayya da sanarwar da hukumar zabe INEC ta fitar a ranar 16 ga watan Afrilun 2022, kan babban zaben shekarar 2023, tuni Jam’iyyar ta PRP ta fitar da ka’idojin sayar da takardun tsayawa takarar ta.
Yace Jam’iyyar zata sayar da takardun tsayawa takarar ta ne kamar haka: Majalisar Dokokin Jiha-Naira 100,000 sai Majalisar wakilai ta tarayya- Naira 250,000 yayin da Majalisar Dattawa kuma – Naira miliyan 1 da 500,000 da na Gwamna-Naira miliyan 2 da 500,000 sai kuma shugaban Kasa-Naira miliyan 10.
“Sanarwar ta kuma yi karin hasken cewa duk wanda zai sayi takardar tsayawa takara sai ya biya kaso biyar (5%) cikin 100 na kudin takardar (Form) a matsayin kudin na gani ina so (expression of interest form).
“Dukkan masu bukata ta musamman dake neman takarar za a basu takardun tsayawa takarar kyauta kuma baza su biya kudin na gani ina so ba.
“Kazalika dukkan Yan takarkaru Mata su kuma zasu biya kaso hamsin (50%) ne cikin 100 na kudaden sayan takardun da kuma na nuna sha’awar tsayawa takarar.”













































