Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa, Barau I. Jibrin ya ja hankalin al’ummar musulmi da su ci gaba da gudanar da ayyukan kirki da suka koya a lokutan azumin watan Ramadana.
Barau ya bayyana hakan ne, ta cikin sakonsa na barka da Sallah da ya fitar a ranar Lahadi.
“Musulmi su yi kokari wajen kiyaye ayyukan alheri da aka gudanar a lokacin azumi, tare da nisantar duk wata alfasha da suka kaurace musu a cikin watan Ramadan mai alfarma,” inji shi.
Yace bai kamata a yi kasa a gwiwa ba wajen dabbaka sunnar hakuri da tsoron Allah da karamci da son juna tare da riko da gaskiya da rikon amana.
Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da kasafin kudi ya bayyana cewa ya kamata a yi amfani da lokutan bayan watan Ramadan wajen kiyaye koyarwar Annabi Muhammad ta fuskar gaskiya da zaman lafiya, da kaunar juna.
Ya ce da tsoron Allah ne musulmi za su iya yin fice da kuma samun gagarumar nasara, a dukkan al’amuran rayuwa.
Mai neman tsayawa taakaarar gwamnan jihar Kano ya kuma yi fatan alheri ga masu hannu da shuni a Kano da su taimakawa marasa galihu da kayan abinci, da sauran kayan masarufi.
Da yake martani kan zaben shekarar 2023, Sanata Barau ya bukaci jama’a da su kara kaimi wajen gudanar da addu’o’in samun ingantaccen tsaro a kasar nan da ka iya kawo cikas ga harkokin zabe.













































