Abuja: Rundunar Soja ta tabbatar da tashin Bom a kusa da Barikin Mogadishu

nigerian army training
nigerian army training

Sojojin a birnin tarayya Abuja sun tabbatar da rahoton samun fashewar wani abu a kusa da barikin soji a birnin na Abuja.

Lamarin ya faru ne a barikin sojoji na Mogadishu da ke kan hanyar Mararaba-Nyanya.

Rundunar sojin ta bayyana hakan ne ta shafinta na sada zumunta ta na mai cewa, lamarin ya afku ne a wata madakatar ababen hawa da ke daura da bakirin ma Mogadishu, inda aka shawo kan lamarin kuma za su fitar da cikakken rahoto a nan gaba.

Rahotonni sun bayyana cewa, wanda ya tayar da bam ɗin ya mutu, yayin da aka samu jikkatar mutum guda inda yanzu haka ya ke samun kulawa a asibitin sojojin.

Sojojin sun ce an shawo kan lamarin zuwa yanzu, tare da cewa babu wata fargaba don haka mutane su kwantar da hankalinsu.

A nata bangaren, rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, ta bakin mai magana da yawunta SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ita ma ta ce, suna gudanar da kwakkwaran bincike a kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here