Baturen ƴan sanda watau DPO da kuma ƙarin wani mutum daya sun mutu sakamakon tashin hankalin da ya barke a karamar hukumar Rano a Kano.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Litinin, mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta SP Abdullahi Haruna Kiyawa.
A cewar sanarwar, rikicin ya fara ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Mayu, bayan da aka kama wani bakaniken babur mai suna Abdullahi Musa bisa zargin tukin ganganci da hatsari.
Sanarwar ta ce ana zarginsa da yin amfani da wasu abubuwa kuma an tsare shi a ofishin ‘yan sandan na Rano.
Haka kuma, a cewar Sanarwar, daga baya ya nuna alamun rashin lafiya kuma an garzaya da shi babban asibitin Rano, inda ya rasu a safiyar ranar Litinin.
SolaceBase ta ruwaito cewa, bayan mutuwarsa, rundunar ‘yan sandan ta ce wasu bata gari ne suka kai hari ofishin ‘yan sanda na Rano, inda suka yi awon gaba da wasu kayayyakin ofishin tare da kona motoci biyu.
“Sun kuma lalata wasu motoci guda goma tare da raunata DPO wanda aka garzaya da shi asibitin koyarwa na Aminu Kano, amma daga baya ya rasu.”
Sanarwar ta kuma ce, an kama mutane 27 da ake zargi da hannu a harin, yayin da aka samu dawowar zaman lafiya a yankin.
Kwamishinan ‘yan sanda na Kano Ibrahim Bakori, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru inda ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Rano, Ambasada Mohammed Isah Umar (Autan Bawo 19).
Haka kuma Kwamishinan, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike na gaskiya don gano musabbabin faruwar lamarin tare da tabbatar da an yi adalci.
Yayin da take jajantawa iyalan marigayi DPO, rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankalinsu, su guji daukar doka a hannunsu.
Sannan kuma ta bai wa jama’a tabbacin tabbatar da zaman lafiya da kare lafiyar al’umma a fadin jihar tare da yin kira ga al’umma da su ba da cikakken hadin kai wajen gudanar da bincike.













































