Jami’an Saudiyya sun hana Shiek Gumi shiga kasar don yin aikin Hajji

Sheikh Gumi 750x430

An fitar da fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi daga kasar Saudiyya bayan an hana shi shiga Madina, inda aka hana shi damar fara gudanar da aikin Hajjin bana.

Sheikh Gumi, wanda mazaunin garin Kaduna ne da ya shahara a kan ra’ayoyinsa masu janyo cece-kuce kan al’amuran kasa da kasa, ya tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin.

Malamin wanda ke cikin tawagar malaman addini da hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON ta dauki nauyinsa, ya isa filin jirgin sama na Yarima Mohammad Bin Abdulaziz da ke birnin Madina a daren ranar Asabar ta jirgin kamfanin Umza.

Sai dai kuma da isar sa jami’an shige da fice na Saudiyya suka tare shi a filin jirgin inda suka hana shi shiga cikin birnin, kafin daga bisani suka sanya shi a jirgin da zai dawo Najeriya.

Sheikh Gumi ya kara da cewa a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin nasa, mahukuntan Najeriya sun nuna damuwa tare da yin alkawarin tattaunawa da mahukuntan Saudiyya domin neman karin haske da kuma warware matsalar.

Wata majiya a hukumar ta NAHCON da ta bukaci a sakaye sunanta ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, hukumar ta yi mamakin matakin da Saudiyya ta dauka, musamman ganin cewa dukkan mambobin tawagar sun samu takardar izinin shiga kasar domin yin aikin Hajji kuma sun cika ka’idoji.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here