Nnamdi Kanu ya nemi afuwa bisa rashin da’a da ya yi a kotu, ya musanta zargin ta’addanci

Nnamdi kanu 750x430

Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu ya nemi afuwar mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da kuma Cif Adegboyega Awomolo, SAN kan rashin da’a da ya yi a shari’ar karshe da aka yi masa kan zargin ta’addanci.

Kanu ya roki gafarar kuma ya yi alkawarin cewa zai kasance da kyawawan halaye a tsawon lokacin shari’ar da ake yi masa.

Neman afuwar na kunshe ne a cikin wani dogon jawabi da babban lauyansa kuma tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Mista Kanu Agabi ya gabatar.

Kanu, musamman ya roki mai shari’a Nyako da Awomolo da su gafarta masa su manta da bacin ransa da ya kai musu hari a fili.

Agabi ya ce Kanu yana da dalilin yin fushi amma bai kamata ya yi magana ba lokacin da fushi ya mamaye shi.

Har ila yau, yayin da ake tuhumar sa a gaban kotu a ranar Juma’a, shugaban na IPOB, ya ki amsa laifin ta’addancin da gwamnatin tarayya ta yi masa.

An gurfanar da shi ne a gaban mai shari’a James Kolawole Omotosho cikin tsananin matakan tsaro da jami’an tsaro na farin kaya (DSS) suka bayar.

Da aka karanta tuhume-tuhume guda 7 daya bayan daya, Kanu, ya musanta zargin yin barazana ga Najeriya da kuma gudanar da gidan rediyon ba bisa ka’ida ba wajen yada sakonnin Biafra.

Bayan karar, lauyan gwamnatin tarayya, Awomolo, SAN ya bayyana wa kotun cewa a shirye yake ya gudanar da shari’a daidai da wasikun kotun koli da ta bayar da umarnin sake shari’ar.

Ya bukaci da a dage shari’a domin ya samu damar hada shaidun sa sannan kuma ya nemi a kara sauraron karar da kotu ta bayar.

Dangane da bukatar da kuma rashin nuna adawa da lauyan wadanda ake karewa karkashin jagorancin Agabi, Mai shari’a James Omotosho ya sanya ranar 29 ga Afrilu da 2 da 6 ga Mayu, 2025 don gudanar da cikakken shari’a

Kanu, wanda aka dawo da shi kasar a watan Yunin 2021 daga kasar Kenya, tun daga lokacin yana hannun hukumar DSS bisa umarnin kotu, ya kuma amince da gaggauta shari’ar tuhumar da ake masa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here