Kotun koli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar PDP

Samuel Anyanwu PDP 750x430

Kotun Kolin kasar nan ta soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta zartas a baya, na dakatar da na hannun damar Nyesom Wike Sanata Samuel Anyanwu, a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na kasa.

A wani hukunci da alkalan kotun mutum biyar suka yanke da mai shari’a Jamilu Tukur ya gabatar, kotun Kolin ya soki kotun ɗaukaka ƙara da babban Kotun jihar Enugu na shiga abin da ta kira rikicin cikin gida.

Tun a baya babbar kotun da ke Enugu ts cire Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar bisa ƙarar da wani ɗan jam’iyyar PDP Mista Aniagu Emmanuel ya shigar.

Hakazalika kotun ɗaukaka ƙara a jihar ta tabbatar da hukuncin babban kotun wanda ta amince da Cif Udeh-Okoye a matsayin wanda ya maye gurbin Sanata Anyanwu a matsayin sakataren Jam’iyya.

Bayan rashin amincewa da hukuncin, Anyanwu ya ɗaukaka ƙarar zuwa kotun ƙoli.

Anyanwu da Sunday Ude-Okoye sun soma rikici kan matsayin sakataren jam’iyyar ne tun bayan da Anyanwu ya bar matsayin domin yin takara a zaɓen gwamnan Imo wanda ya yi rashin nasara.

Bayan rashin nasararsa, ƙoƙarin dawowa kan kujerarsa ya jefa jam’iyyar cikin rikici wanda ya kawo rarrabuwar kai tsakanin ƴan ƙungiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here