Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane goma da ake zargi da yin garkuwa da mutane da fashi da makami, inda ta kwato kimanin Naira miliyan 5 na kudin fansa da bindigogi, da alburusai.
Kamen dai ya biyo bayan tsaurara matakan tsaro da sabon kwamishinan ‘yan sandan da aka nada, CP Ibrahim Adamu Bakori wanda ya fara aiki a ranar 17 ga watan Maris ya yi.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce an dauki matakin ne bisa umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasa IGP Kayode Adeolu Egbetokun, inda ya bukaci ‘yan sandan da su kara karfafa ayyukan leken asiri a fadin kasar.
A cewar Kiyawa, jerin ayyukan hadin gwiwa sun kai ga cafke wasu da dama da ake zargi da aikata laifukan ta’addanci a fadin Kano.
Karanta: Gwamnan Kano ya amince da karin albashi ga ma’aikatan manyan makarantu
Daga cikin su akwai wasu mutane biyu da aka kama da hannu a wani fashi da makami a Layout Badawa.
Hakazalika, an kama wani dan fashi da makami mai shekaru 25, Shuaibu Yakubu, wanda ake kira da Dan Bula Bula, dauke da bindiga kirar AK-47 da alburusai 12 da kuma motar Pontiac Vibe da ya sace.
Wanda ake zargin ya amsa laifukan fashi da makami a Kano da Abuja.
A wani samame kuma, jami’an ‘yan sanda sun kama Friday Bitrus mai shekaru 38 da kuma Daniel Samuel mai shekaru 25 a Zango Quarters Kano, inda suka kwato wata karamar bindiga da aka kera ta gida da harsassi masu rai guda biyu, da gatari.
Al’amarin da ya fi daukar hankali shi ne ceto wani da aka yi garkuwa da shi, Muhammad Bello, mai shekaru 21, daga Garin Zakirai da ke karamar Hukumar Gabasawa.
Rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da farmakin ne ta hanyar leken asiri bayan iyalansa sun kai rahoton sace shi da kuma neman kudin fansa naira miliyan 15.
A tsakanin ranakun 11 zuwa 18 ga watan Maris, jami’an tsaro sun kama mutane biyar da suka hada da mata biyu, tare da kwato bindigar Dan kasar Denmark tare da Naira miliyan 4.85 na kudin fansa.
Dukkan wadanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.