Kotu ta dakatar da INEC daga karbar koke na dawo da Natasha Akpoti

Natasha Akpoti Uduaghan 720x430

Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Lokoja Jihar Kogi, ta ba da umarnin wucin gadi na hana hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ds ma’aikatanta, ko wakilai daga karba, ko karba, ko aiki da duk wata kara da ke dauke da sa hannun ‘yar majalisar dattawa daga Kogi ta Tsakiya wadda aka dakatar.

Umarnin ya kuma hana INEC gudanar da duk wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a dangane da irin wannan bukata ta neman a fara shirin dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Umurnin dai ya biyo bayan wata takardar neman izinin wucin gadi ne, wanda ya samu goyon bayan wata takardar gaggawa da kuma wasu tsare-tsare na kotu da Anebe Jacob Ogirima ya sanya hannu a madadinsa da wasu masu kara guda hudu, wadanda dukkaninsu sun kasance masu rijistar zabe da mazabar Kogi ta tsakiya.

A hukuncin da ya yanke, alkalin kotun mai shari’a Isa H. Dashen, a kara mai lamba FHC/LKJ/CS/13/2025, ya ce:

Umurnin wucin gadi da ya hana wanda ake tuhuma (INEC), ma’aikatansu, wakilai, ko ba da izini daga karba ko yin aiki ta kowace hanya a kan duk wani koke da wani mutum ko mutane za su gabatar da ke dauke da sa hannun karya da sunan ‘yar majalisar dattawan Kogi ta tsakiya.

Karin karatu: Yan sanda sun kama mutane 10 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, fashi da makami a Kano

Umarnin ya kuma hana INEC gudanar da duk wata kuri’ar raba gardama kan irin wannan koke da nufin fara shirin dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, har zuwa lokacin da za a yanke shawarar gabatar da kudirin.

Daga baya kotun ta ba da umarnin kamar haka: An ba da umarnin wucin gadi. Cewa ranar dawowar zata kasance Mayu 6, 2025.

A farkon makon nan ne dai aka fara nuna damuwa dangane da shirin da ake shirin yi na kiranyen wanda ake zargin wani na hannun daman shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya dauki nauyinsa.

Ana zargin shugaban majalisar dattawan da laifin Neman yin lalata da sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here