Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyar da masu tsaron al’umma uku

Bandits 750x430

Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyar da masu gadin al’umma uku a lokacin da suke sintiri a kan hanyar Gusau zuwa Funtuwa da ke cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin mai suna Ya’u Musa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin Alhamis lokacin da jami’an tsaron ke sintiri a kusa da garin Gidan-Giye, kilomita kaɗan daga garin Tsafe, hedkwatar ƙaramar hukumar.

Ya ce ‘yan bindigar sun fito daga ɓoyayyen wurinsu suka bude musu wuta kwatsam.

Musa ya ce duka jami’an tsaron da ke cikin motar suka mutu nan take bayan harin, inda ake zargin cewa ‘yan bindigar sun samu bayanin motsinsu daga wasu masu basu labari.

Jami’an da abin ya shafa an ce sun fito ne daga fadar gwamnati ta Gusau domin taimaka wa matafiyan da ke fuskantar hare-hare a wannan hanya.

A cewar shaidar, bayan sun kashe jami’an, ‘yan bindigar suka hau babura suka tsere cikin daji kafin a samu taimako.

Yanzu haka dai Gawar waɗanda suka mutu an kai su Cibiyar Kula da Lafiya ta Ƙasa da ke Gusau, domin ci gaba da bincike da adana su.

Gwamna Dauda Lawal ya mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa, inda ya nuna bakin cikinsa kan wannan mummunan lamari.

Ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa waɗanda suka rasu, ya kuma bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.

Gwamnan ya kuma sake roƙon Allah da ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar jihar Zamfara, arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here