Gwamnatin jihar Kano ta amince da karin kashi 25 cikin 100 da kashi 35 na albashi ga ma’aikatan ilimi da na manyan makarantu, daga watan Maris na 2025.
Kwamishinan yada labarai Abdullahi Waiya ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a Kano.
Waiya ya ce shawarar ta amince da muhimmiyar rawar da ma’aikatan ke takawa wajen ciyar da bangaren ilimi gaba da ci gaban makarantu baki daya.
Ya kara da cewa gyaran albashin ya kara jaddada kudirin gwamnati na inganta yanayin ma’aikata da kuma tallafawa manyan manufofinta na sake fasalin ilimi.
Karin karatu: Hukumar Nimet ta yi gargaɗi kan ɓullar cutar sanƙarau a Najeriya
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 domin gudanar da ayyukan raya kasa daban-daban a fadin jihar.
Ya ce an ware Naira miliyan 148.9 domin kula da hanyoyin sadarwa a makarantar Fasaha da hukumar kula da gyaran titinan Kano (KARMA).
Bugu da kari, an amince da Naira miliyan 367.9 a matsayin kudin ci gaba da aikin fadada hanyar Zaria, daga Silver Jubilee zuwa Dantata & Sawoe.
Majalisar ta kuma amince da Naira miliyan 612.4 don sauya kayayyakin wutar lantarki na waje zuwa tsarin karkashin kasa a gidan gwamnati da kuma mayar da layukan wutar lantarki a hanyar Ahmadu Bello.
An saki Naira miliyan 184 na motocin daukar marasa lafiya guda biyu na asibitin gidan gwamnati da kuma Nuhu Bamalli.
Waiya ya kuma ce an ware Naira miliyan 348 don daidaita kudaden makamashi ga KEDCO na watan Nuwamba da Disambar 2024.
Ya ce an saki Naira miliyan 662 domin ciyar da dalibai a makarantun kwana a sati na 3 zuwa 5 na zangon karatun da ake ciki.
Bugu da kari kuma, an amince da Naira miliyan 100 ga kungiyar ’yan fansho don karbar bakuncin taron wakilanta na shekara hudu a Kano. (NAN)