Kungiyar gwamnonin Kudu-maso-Kudu ta bayyana damuwarta kan ayyana dokar ta-baci ta tsawon watanni shida a jihar Rivers da kuma dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa, inda suka yi kira da a sake duba matakin.
S wata sanarwa da shugaban kungiyar, Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya sanya wa hannu, kungiyar ta amince da alhakin da kundin tsarin mulki ya rataya a wuyan shugaban kasa na tabbatar da doka da oda a fadin kasar nan.
Sai dai sun sanya ayar tambaya kan ko halin da ake ciki a jihar Rivers ya dace da matakin da kundin tsarin mulkin kasar ya shimfida na yin irin wannan sanarwar.
Da suke ambaton sashe na 305 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya (kamar yadda aka yi masa kwaskwarima), gwamnonin sun lura cewa, ya kamata a sanya dokar ta-baci ne kawai a cikin da aka shiga matsanancin yanayi, kamar yaki, wuce gona da iri, ko kuma tabarbarewar zaman lafiyar jama’a.
Karanta: Tinubu ya yaba wa majalisa bisa tabbatar da dokar ta-ɓaci a Rivers
Sun yi nuni da cewa rigingimun siyasa a jihar Rivers bai dace da dakatar da hukumomin da dimokuradiyya ta zaba ba.
Bugu da kari, kungiyar ta jaddada cewa kundin tsarin mulkin kasa ya tanadi kwararan matakai na tsige gwamna, mataimakin gwamna, da ‘yan majalisar wakilai a karkashin sashe na 188.
Gwamnonin sun nuna damuwarsu kan cewa watakila ba a yi amfani da wadannan tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ba a halin da ake ciki.
Domin kwantar da tarzoma da samar da zaman lafiya mai dorewa, kungiyar gwamnonin Kudu-maso-Kudu ta bukaci Gwamnatin tarayya da ta janye dokar ta-baci ta kuma ba da damar tsarin mulki da na doka don warware rikicin siyasa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar Rivers.
Kungiyar ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankula, su kiyaye doka, su rungumi tsarin tattaunawa a matsayin hanyar da za a bi a warware matsalar.