Hukumar kashe gobara ta tarayya (FFS) ta tabbatar da cewa mutane biyu sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da aka yi a gadar Karu da ke kan titin Abuja-Keffi—inda aka samu mummunar fashewar wani abu ranar Laraba, inda yanzu haka aka tabbatar da mutuwar mutane 10.
Shugaban hukumar kashe gobara ta tarayya Engr. Jaji O. Abdulganiyu, wanda ke wajen da lamarin ya faru, ya tabbatar da cewa tuni an aiwatar da matakan da suka da ce.
“Wata motar tirela dauke da taki ta rasa birki, inda ta kife tare da rufe babbar hanyar, abin bakin cikin ma shi ne an rasa rayuka biyu nan take, wasu motoci da dama sun lalace.
“Yayin da tawagar ta sanar da tashar kashe gobara mafi kusa don daukar matakin gaggawa, an gano wani hatsarin da ke kunno kai – wata tankar mai dauke da man fetur ta fara zubar da man cikinta a cikin wasu motocin da ke karkashin rana mai zafi. Da sauri ma’aikatan kashe gobara na tarayya suka yi amfani da kumfa don shawo kan matsalar da kuma hana afkuwar bala’i,” in ji hukumar.
Karanta: Gwamnonin Kudu-maso-Kudu sun bukaci a janye dokar ta-baci a Rivers
A wani labarin kuma, Hukumar ba da sgajin gaggawa ta babban nirnin tarayya (FEMD) ta tabbatar da cewa mutane 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar wata babbar mota da ta afku a gadar Karu a ranar Laraba.
Shugaban sashin kiran gaggawa FEMD, Mark Nyam ne ya bayyana hakan yana mai cewa: an ajiye gawarwaki takwas a dakin ajiye gawa na Asibitin Karu, sai kuma gawar mutum daya zuwa Asibitin Asokoro.
Sai kuma sama da mutane 30 da abin ya shafa sun samu ƙuna daban-daban, inda aka kai wasunsu zuwa Asibitin Koyarwa na Gwagwalada, ds cibiyar kiwon Lafiya ta tarayya (FMC) Keffi, da Asibitin Cedarcrest, Abuja don samun kulawa.
Akalla motoci 10 ne suka lalace a fashewar.
Shugaban hulda da jama’a na FEMD, Nkechi Isa, ya ruwaito mukaddashin Darakta Janar injiniya Abdulrahman Mohammed, ya bukaci masu ababen hawa da su bi ka’idojin zirga-zirga, da kaucewa tukin ganganci da rashin kula da abin hawa.”