Jack Dorse, Shugaba na 2 a kamfanin sadarwar twitter zaiyi murabus dan baiwa wani dama ya jagoranci kamfanin akaro na gaba.
Kamfanin twitter zai maye gurbin magatakaddar kamfanin da babban jami’i mai kulada sashin fasaha na kamfanin Parag Agrawal a shekara me kamawa.
Shi dai Jack Dorse zai cigaba da jagorantar kamfanin zuwa sabuwar shekara yayin da wa’adin aikin sa a kamfanin zai kare kamar yadda kamfanin twitter ya sanar.
“Na yanke shawar ajiye aiki daga kamfanin domin nayi imanin cewa kamfanin ashirye yake ya dauki sabuwar alkibla daga sauran shugabannin kamfanin dazasu jagoranci tafida kamfanin”
“Kuma na tabbata a shekaru 10 da Parag Agrawal yayi yana hidimtawa kamfanin ba shakka nasan bazai bani kunya ba idan yazamo sabon magatakaddar kamfanin” inji Dorsey (shugaban kamfanin twitter mai barin gado)
Rahotanni sun nuna cewa anasaran shugaban gudanarwar kamfanin Patrick Pichette shima zai ajiye aiki wanda ake saran maye gurbin sa da Bret Tylor wanda ke cikin Daraktocin kamfanin tun a 2016.
“Amadadin hukumar gudanarwar wannan kamfani, Ina mai godewa magatakaddar kamfanin twitter mai barin gado bisa sadaukarwa da goyon bayan da yabani” inji Tylor













































