Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta karbe ragamar karben dukkan kudaden yin rijista na Naira Dari Bakwai Bakwi (700) daga hannun cibiyoyin zana jarabawar dan kawo karshen uzurawa dalibai masu neman zana jarabawar daga shekara me kamawa.
Rahotannin da ke fita cikin jadawalin sanarwar da hukumar keyi kowanne mako tace zata maye karban naira 700 da ake cazar masu neman zana jarabawar, inda daga bisani hukumar ta rika aikewa da cibiyoyin jumullar kudaden.
“Hukumar jamb daga shekara me kamawa, 2022 ita ce zata cigaba da karban kudin yin rijista da ta amince dasu naira 700 amadadin cibiyoyin da dalibai ke zana jarabawar.”
“Hukumar bayan tara kudaden zata aike tareda maida adadin kudaden kai tsaye zuwa ga bankunan ajiya na kowacce cibiya kowanne mako ko kuma duk lokacin da cibiyoyin suka amince da shi”
“Kuma daukar wannan mataki na da alaka da wasu yan kura_kurai dakê faruwa nan_da_can awasu cibiyoyi da hukumar bata amince dasu ba, kasancewar an kayyade naira 700 ne kacal amma wasu cibiyoyin nayin abinda sukaga dama ta hanyar gallazawa dalibai biyan kudaden da suka haura tunani” inji Jamb
Hukumar daganan tace, sauye sauye kuma bazai canza adadain kudin rijista zana jarabawar ba, face dai kawai kowanne dalibi zaije cibiyoyin yayi rijista batareda biyan komai ba, kasancewar za a sanya naira 700 ne yayin biyan kudin sayen lambobin sirri nayin rijistar jarabawar.
Rahotanni da ke fitowa daga hukumar nacewa daukar wannan mataki nazuwane adaidai lokacin aka Sami kididdigar takaddun shedar shiga wata makarantar gaba da sakandire kimanin 146, Inda binciken yanuna sakamako 6 ne kacal hukumar ta iya tantance ingancin su.













































