Shell zai biya mazauna Neja-Delta diyyar yuro miliyan 15

fb3b2437 8da2 451b 97a8 9da4865cb120
fb3b2437 8da2 451b 97a8 9da4865cb120

Kamfanin haƙar ɗanyen man fetur na Shell zai biya diyyar yuro miliyan 15 (dala miliyan 15.9) ga mazauna yankin Neja-Delta a kudancin Najeriy waɗanda malalar man fetur ta shafa.

Alƙawarin biyan diyyar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a tare da haɗin gwiwar reshen cibiyar Friends of the Earth a ƙasar Netherlands.

Matakin ya biyo bayan hukuncin kotun Netherlands inda ta kama reshen kamfanin na Shell a Najeriya da laifin malalar mai a shekarar da ta wuce kuma ta umarci Shell ya biya diyya.

Tun a shekarar 2008 manoma daga Neja-Delta tare da taimakon Friends of the Earth suka gurfanar da Shell a gaban kotun da ke The Hague sakamakon gurɓata musu muhalli da ya yi a tsawon shekarun da ya shafe yana haƙo albarkatun fetur a yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here