Rikici ya barke a ƙungiyar Lauyoyi NBA yayin da kotu ta dakatar da zaben 2026

NBA

Rikicin da ke addabar shugabancin kungiyar lauyoyin Najeriya NBA ya dauki sabon salo bayan babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan ta bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da kungiyar daga ci gaba da shirya zaben manyan shugabanninta na kasa na shekarar 2026.

A hukuncin da mai shari’a G. A. Opayinka ya yanke, kotun ta amince da bukatar da aka shigar ba tare da sauraron bangare na biyu ba, inda ta hana mambobin kwamitin zabe na kungiyar lauyoyin Najeriya ECNBA su ci gaba da bayyana kansu a matsayin jami’an kwamitin ko daukar duk wani mataki da ya shafi shirya zaben, har sai an yanke hukunci kan bukatar umarnin dakatarwa da aka tsara sauraron ta ranar 12 ga Maris.

Kotun ta kuma hana shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya Maxi Afam Osigwe SAN da sauran wadanda ake kara daga daukar duk wani mataki na kafa kwamitin zaben ECNBA ko shiga, sa ido, tasiri ko katsalandan ta kowace hanya a gudanar da zaben shugabannin kasa na shekarar 2026 har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu.

An shigar da karar mai lamba 1/221/2026 ne daga wasu lauyoyi guda hudu da suka hada da Ibrahim Lawal, Raymond Oki, Omotan Olusola Ogunmodede da kuma Chief Gabriel Ojo Adekunle Ijalana.

Masu ƙarar sun shigar da ƙarar ne a kan shugaban ƙungiyar lauyoyin Najeriya tare da sanya amintattun wakilan ƙungiyar da aka yi wa rajista, majalisar manyan lauyoyi masu kula da harkokin ɗabi’ar aikin lauya, babban lauyan gwamnatin tarayya a matsayinsa na shugaban majalisar kula da harkokin lauyoyi ta ƙasa, da kuma wasu mutane da suka haɗa da Aham Ejelam babban lauya na Najeriya, Ibrahim Aliyu Nasarawa, Mohammed Nuhu, Uju Okafor da Ume Maduka a matsayin waɗanda ake ƙara tare.

Masu karar na kalubalantar sahihancin tsarin zaben da kuma rawar da shugabannin kungiyar lauyoyin Najeriya suka taka wajen kafa kwamitin zaben.

A cikin makonni biyu kacal, wannan shi ne karo na biyu da kotu ke shiga cikin batun zaben kungiyar, domin a baya wani alkali na babbar kotun jihar Oyo da ke Ibadan ya bayar da umarnin wucin gadi a wata kara mai lamba I/205/2026 da amintattun wakilai na Egbe Amofin O’odua suka shigar.

A wancan hukuncin, kotun ta hana kungiyar lauyoyin Najeriya da wakilanta amincewa ko karbar takarar duk wani dan takara da ba na hadin gwiwar kungiyar lauyoyin Yarabawa ba domin kujerar shugaban kungiyar a zaben 2026 har sai an kammala sauraron bukatar da ke gaban kotu.

Umarnin da aka bayar ranar 24 ga Fabrairu ya dakatar da tsarin karbar ‘yan takarar shugaban kungiyar da ba su cikin tsarin hadin gwiwar da kungiyar lauyoyin Yarabawa ta gabatar, yayin da sabon umarnin da aka bayar ranar 4 ga Maris ya dakatar da aikin kwamitin zaben gaba daya.

Hakan ya haifar da rashin tabbas kan yadda za a gudanar da zaben kungiyar lauyoyin Najeriya na shekarar 2026 da kuma jadawalin lokacin zaben.

Shari’ar na zuwa ne a lokacin da ake fama da rikici kan shugaban kungiyar, bayan wasu manyan lauyoyi sun nuna damuwa kan zargin rabon wasu kudade da ba a bayyana su ba ga wasu mambobin kungiyar a wani taro na hukuma da aka gudanar a Maiduguri.

Wannan rikici ya haifar da rabuwar kai a tsakanin lauyoyi, inda wasu ke bukatar cikakken bayani da daukar matakin hukuma, yayin da wasu ke ganin zargin yana da alaka da siyasa.

Masu sukar lamarin sun bayyana cewa zargin karbar kudade da rabon su ga wasu mutane kadai, wadanda aka ce kudaden kasashen waje ne, ya saba da dokokin kungiyar lauyoyin Najeriya da suka bukaci bayyana duk wani kyauta da aka karba a irin wadannan taruka.

Rikicin ya kara tsananta bayan wasu kalamai da ake dangantawa da shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya kan sahihancin bangaren shari’a, wanda wasu manyan lauyoyi suka bayyana a matsayin kalamai marasa dacewa.

Yayin da magoya bayan shugaban kungiyar ke cewa babu wani laifi da aka tabbatar kuma dole a bi doka da ka’ida, masu adawa da shi na cewa yawan zarge-zargen da ake yi ya rage amincewa da sahihancin tsarin zaben, wanda hakan ya sa kotu ta shiga lamarin.

Da yake yanzu tsarin karbar ‘yan takara da kuma ikon kwamitin zaben duka suna karkashin umarnin kotu, akwai yiwuwar jadawalin zaben kungiyar lauyoyin Najeriya na shekarar 2026 ya fuskanci cikas.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here