Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwanso, ya ayyana tsayawa takararsa ta shugabancin kasa a babban zaben shekarar 2023 a hukumance.
Tsohon Ministan tsaron ya sayi Form din tsayawa takara da kuma nuna sha’awarsa ne karkashin inuwar Jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso bayan biyan kudin Fom din ya bukaci ‘Yan Najeriya musamman yan siyasar dake da burin kawo sauyi a kasar nan kan su shiga Jam’iyyar ta NNPP.
Da yake jawabi Yayin da yake karbar Fom din tsayawa takarar a Shalkwatar Jam’iyyar ta NNPP dake Abuja, Kwankwaso yace yana sa ran Jam’iyyar tasu ta NNPP zata karbi shugabancin Najeriya a shekarar 2023.
“Wannan jam’iyya ce mai son sauya yanayin siyasar kasar nan, wadda ke da burin kawo ci gaba mai dorewa, ko wacce unguwa a yanzu idan ka ziyarceta babu jam’iyyar da mutane ke magana a kai face Jam’iyyar NNPP.
“Mu mutane ne masu son hada kan kasar nan ba tare da la’akari da addini da kabila ba domin kasar ta mu ce baki daya,” inji Kwankwanso.













































