Jirgin saman horar da sojojin saman Najeriya (NAF) ya yi hatsari da yammacin ranar Talata tare da matukan jirgin biyu.
Jirgin mai suna Super Mushak, ya yi hatsarin ne a Kaduna a lokacin da yake wani atisayen horo.
Rahotanni na nuni da cewa matukan jirgin da ke cikin jirgin sun mutu.
Wata majiya ta bayyana cewa jirgin ya fado ne a cikin harabar sansanin Sojin saman da ke jihar Kaduna.
Wannan dai na zuwa ne watanni 11 bayan da wani jirgin rundunar Sojin Saman ya yi hatsari a Kaduna wanda ya yi sanadiyar mutuwar babban hafsan sojin kasa na lokacin Ibrahim Attahiru da wasu jami’an soji 10.











































