Babban sifeton ƴan sandan Najeriya Usman Baba, ya tabbatar da naɗin CSP Olumuyiwa Adejobi, a matsayin jami’in hulda da jama’a na 25.
An tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da sufeto Anjuguri Manzah, jami’in gudanarwa na sashen hulɗa da jama’a na rundunar, ya fitar da yammacin yau Talata.
An naɗa CSP Adejobi a matsayin muƙaddashi a ranar 16 ga Fabrairun bana bayan ya karɓi mukamin CP Frank Mba, wanda babban sufeton ƴan sanda ya zaɓa a matsayin babban kwas na zartarwa a Cibiyar nazarin manyan buƙatu ta ƙasa NIPSS da ke Kuru. Jos.
CSP Adejobi ya karanci Archeology da kuma Geography a Jami’ar jami’ar Ibadan.
Ya yi karatun digiri na biyu a fannin zaman lafiya da rikice-rikice a dai wannan jami’a.
Haka kuma ya taɓa riƙe muƙamin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda a jihar Ogun daga shekarar 2008 zuwa 2016, sannan ya yi aiki a shalkwatar shiyya ta biyu da ke Onikan a jihar Legas a shekarar 2016 a matsayin jami’i hulɗa da jama’a, kana ya yi aiki a rundunar ƴan sandan Jihar Legas tsakanin watan Satumba shekerar 2020 zuwa Agustan bara 2021, lokacin da aka ayyana a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon kakakin rundunar na ƙasa CP Frank MBA.
Ya kuma yi aiki a matsayin jami’in Ayyuka, a sashen yaƙi da ƴan fashin Banki da kuma hana fasa bututun a mai Sagamu Division daga shekarar 2006 zuwa 2008, haka kuma ya yi aiki a sashen gudanarwa shalkwatar ƴan sanda ta Jjihar Ogun a shekarar 2008 sai kuma aiki a sashen ayyuka na rundunar ƴan sandan jihar Legas, a shekarar 2017.













































