Mai neman takarar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin jam’iyyar APC Sha’aban Ibrahim Sharada, ya bayyana zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan jihar a matsayin wani aiki da aka tafka kura-kurai, sayen kuri’u da kuma tsoratarwa.
Don haka ne Sha’aban Sharada ya ce, bai amince da sakamakon zaben fidda gwanin da aka yi ba, kuma ya buƙaci da a soke zaɓen.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa an gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC ranar Alhamis a filin wasa na Sani Abacha.
Sharada, ɗan majalisar tarayya, kuma shugaban kwamitin majalisar wakilai na tsaro da leƙen asiri, a wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, ya bayyana cewa a yayin da ake ci gaba da gudanar da zaɓen fidda gwanin, cikin ikon Allah ya tsallake rijiya da baya daga wurin zaɓen fidda gwanin.
“Na tsallake rijiya da baya bisa wani yunkurin kisa, a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar mu na gwamna da ya gudana a Kano, Mintuna kaɗan da fara aikin, jami’an tsaro suka gargaɗe ni da cewa kada na zo wurin da za a yi zaɓen, a lokaci guda kuma na samu sakon kar ta kwana daga shugaban kwamitin zaben fidda gwani a gaban Sanata Tijjani Kaura yana kira na. su kasance a wurin da za a fara zaben”.
“Abin da ya ba ni mamaki, an nemi jami’an tsaron da aka turo daga Abuja don bani kariya da su tafi wurin da za a gudanar da zaɓen,” in ji Sharada a cikin sanarwar da ya fitar.
Ya ƙara da cewa an kai wa da yawa daga cikin magoya bayansa hari kuma a cikin haka ne wasu daga cikinsu suka rasa rayukansu.
“Yayin da ake ci gaba da zaɓen, akwai wasu tsare-tsare na amfani da ƴan daba da kuma kawo ƙarshen rayuwata a lokacin da nake fitowa daga wurin taron, Daga baya ma na samu wani rahoton sirri na cewa waɗannan ƴan barandan sun riga sun kai hari har sun kashe da kuma raunata dimbin magoya bayana wanda hakan ya sa na yi gaggawar ficewa daga wurin taron na wuce asibiti inda ake kula da lafiyarsu, Don haka a gare ni ran mutum ɗaya ya fi daraja a kan siyasa da kuma zama Gwamna,” inji shi.
“Don haka, ina kira ga jami’an tsaro da babbar jam’iyyar mu da su yi bincike da gaske tare da hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da gaggauta soke zaɓen fidda gwanin da aka tafka kura-kurai, sayen kuri’u da kuma tsoratarwa, hakan ba ya nuna manufar babbar jam’iyyarmu da dimokuradiyya ta gaskiya, Yayin da yake tabbatar wa dandazon magoya bayanmu cewa za mu ci gaba da fafutukar kwatowa da dawo da martabar jiharmu, wannan yunkurin ba zai sanya ni karaya ba na dakatar da ayyukan alheri da muke yi.” Inji shi.












































