Kwamitin zartaswa NWC na jam’iyyar Social Democratic Party SDP, ya dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Alhaji Shehu Musa Gabam da mai binciken kudi na kasa Nze Nnadi Clarkson, da shugaban matasa na kasa Uchechukwu Chukwuma.
An dakatar da shugaban jam’iyyar SDP na kasa din ne biyo bayan kudurin wani taro na kwamitin.
Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar ta bayyana cewa, an gabatar da kwararan hujjoji da ke danganta jami’an da aka dakatar da wasu makudan kudade da ba su da izini da tsare-tsare na inganta rayuwar jama’a, da kuma fitar da kudade daga asusun jam’iyyar ba tare da amincewar da kwamitin zartaswar na kasa NWC ya yi ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, kamar yadda doka ta 19.1 da ta 19.3(i) da 19.5 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar na shekarar 2022 da aka yi wa kwaskwarima, kwamitin zartaswa na kasa NWC, na jam’iyyar Social Democratic Party SDP, ya amince da dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Alhaji Shehu Musa Gabam, tare da mambobin kwamitin guda biyu.
Clarkson, mai binciken kudi na kasa, da Uchechukwu Chukwuma, shugaban matasa na kasa, bisa manyan zarge-zargen da ake yi na badakalar kudi da almubazzaranci da karkatar da kudaden jam’iyya.”
A cewar sanarwar, matakin da hukumar kwamitin na NWC ta dauka na dakatar da mutanen uku shi ne nuna wa ‘yan Najeriya cewa jam’iyyar.












































