Peter Obi ya ziyarci Shekarau a Abuja

WhatsApp Image 2025 06 24 at 11.51.46 750x430

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi, ya kai wa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ziyara a gidansa da ke Abuja.

Sanata Ibrahim Shekarau, wanda ya taba zama gwamnan jihar Kano karo na biyu, kuma tsohon ministan ilimi, ya kuma kasance dan takarar shugaban kasa a zaben 2011 a karkashin jam’iyyar ANPP, sannan kuma jigo kuma shugaban jam’iyyar League of Northern Democrats LND.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa, a yayin ganawar, shugabannin biyu sun yi wata tattaunawa da ta shafi batutuwan ci gaban kasa.

Duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanai kan tattaunawar tasu ba, ana ganin ziyarar a matsayin wani bangare na kokarin da masu ruwa da tsaki ke yi na tsara hanyar da za a bi wajen samar da hadin kai da ci gaban Najeriya.

Peter Obi dai ya ci gaba da jan hankalin jiga-jigan siyasa da masu ra’ayi a fadin Najeriya tun bayan kammala babban zaben da ya gabata.

Haka kuma, SolaceBase ta ruwaito cewa, a ‘yan watannin nan, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kara kaimi wajen wayar da kan ‘yan jihar da kuma ’yan siyasa, inda ya jaddada bukatar samar da shugabanci na hadin gwiwa da sauye-sauyen manufofin da suka ba da fifiko wajen gudanar da shugabanci nagari da daidaito da kuma farfado da tattalin arziki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here