Ramadan Iftar: Buhari ya karbi bakuncin gwamnonin Jihohin Najeriya 36 a fadarsa

IMG 20220419 WA0186 678x381 2
IMG 20220419 WA0186 678x381 2

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Gwamnonin Jihohi 36 na Tarayyar Najeriya, da shugabannin hukumomin tsaro da shugabannin kungiyoyin sa-kai na soji a fadar gwamnati da ke Abuja, domin shan ruwa tare da su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa tun da farko wasu daga cikin bakin shugaban kasar sun yi Sallar Magriba tare a masallacin Aso Villa kafin a fara buda bakin.

Tun a ranar Alhamis ma 14 ga watan Aprilun 2022 shugaban ya karbi bakuncin shugabannin ma’aikatan shari’a na Najeriya a yayin buda baki na ranar.

A wajen taron buda bakin na ranar Talatar shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa bangaren zartarwa zai ci gaba da mutunta bangaren shari’a kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasar domin karfafa dimokradiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here