Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta nemi gwamnatin tarayya da ta wallafa tareda aiwatar da rahotannin ziyarar ayarin shugaban kasa zuwa jami’o’in tarayya domin magance manyan kalubalen da ke addabar jami’o’i daban -daban.
Shugaban ASUU Shiyyar Kano, Farfesa Abdulkadir Muhammad ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma’a, wanda aka gudanar a Jami’ar Bayero ta Kano.
Karanta Wannan:YANZU-YANZU: Gwamna Sanwo-Olu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Harajin VAT
Ya ce kungiyar ta lura cewa Kwamitin da ya ziyarci Jami’o’in Tarayya ya kammala ayyukan sa, a don haka, kungiyar na kira ga gwamnati da ta hanzarta aiwatar da shawarwarin ta.
Farfesa Muhammad ya zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen cika alkawarun da aka amince da su na MoA, wanda ya kai ga kawo karshen yajin aiki a kasar.
Ya ce kungiyar za ta yi amfani da duk wata hanya da ta dace da doka, don cimma burin ta.
A cewarsa, duk da yake yajin aikin ba shine kawai zabin da kungiyar ke da shi ba, amma shine mafita ta ƙarshe saboda “da alama shine kawai harshe da gwamnati ke fahimta”.
Karanta Wannan: Kere-Keren Kayan Aikin Gona Ne Mafita Ga Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Nan-Parfesa Zilkifili Abdu.
Muhammad ya ce shiyyar, wacce ta kunshi jami’o’i bakwai, a taron ta na ranar Juma’a, ta sake duba matakin aiwatar da MoA na Disamba 2020 ta FG “wanda ya danganci Asusun Tallafa wa Jami’o’in Najeriya, da na kudaden Alawus (EAA) da wasu Batutuwan a Jami’o’in Jihohi.
A cewarsa “Ya kamata‘ yan Najeriya su dora wa Gwamnati alhakin duk wani cikas na kalandar ilimi a Jami’o’in Najeriya.










































