Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya rattaba hannu kan dokar ƙara haraji a jihar.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Mista Gbenga Omotoso, ya fitar a ranar Juma’a, ta ce gwamnan ya rattaba hannu kan kudirin ne bayan ya dawo daga ziyarar aiki.
Karanta Wannan: Kere-Keren Kayan Aikin Gona Ne Mafita Ga Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Nan-Parfesa Zilkifili Abdu.
Sanarwar ta ce, “Gwamnan ya rattaba hannu kan kudirin dokar don sanyawa da kuma cajin VAT kan wasu kayayyaki da aiyuka da misalin karfe 11. 45 na safiyar yau, bayan ya dawo daga ziyarar aiki a Abuja.
Da wannan kudurin yanzu ya zama doka. ”
Za ku ji ƙarin bayani nan gaba….…












































