Masana na bayyana ra’ayin cewa Kere-Keren kayan aikin Gona ita ce Mafita ga bunkasar tattalin arzikin kasar nan.
Farfesa Zilkifili Abdu, Shugaban kwalejin kimiyya da Fasaha ta Hadejia ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Solacebase cewar yanzu Lokaci ya yi da yakamata ace an samu Sabbin kayayyakin aikin Gona na zamani da manoma za su yi amfani da su wajen inganta aikin gona.
Ya ce duk da irin tarin Jami’o’i da kwalejojin Fasaha da kasar nan ke da su, har yanzu manoma na amfani da kayayyakin aikin gona wadanda aka gada shekara da shekaru,kamar su fatanya, garma da dai sauransu. Ya ce Tuni wasu kasashe suka manta da wadancan tsoffin kayayyaki a sakamakon kirkirar Sabbi wadanda suke da sauki gami da sauri wajen aikin Gona.
Karanta Wannan:NITDA ta yi gargadi game da satar bayanai da manhajojin kiwon lafiya ke yi
Farfesa Zilkifili Abdu ya kara da cewar tuni kwalejin Fasaha ta Bilyaminu Dake Hadejia ta yi nisa wajen kere keren irin wadannan kayan aikin gona don saukaka sha’anin ayyukan gona inda a yanzu haka kwalejin ta samar da inginan gyaran shikafa,inginan kyankysar Kwai, da sauran kayayyakin noma.
Kazalika ya yabawa Gwamnatin tarayya wacce ta himmatu wajen ganin an inganta fannonin noma ta fuskar fito da sabbin dabaru a sassa daban daban dake fadin kasar nan. Haka kuma Farfesan ya yabawa Shugaban Hukumar Fasahar Sadarwa ta kasa Kashifu Inuwa bisa Gudummuwar da yake bawa Kwalejin ta fuskar gine gine,kayayyin aiki da kuma na’ura mai kwakwalwa har guda dari biyu(200).
Karanta Wannan: YANZU-YANZU:Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sanar Da Ranar Sake Buɗe Makarantu
Farfesan yace itama Gwamnatin jihar Jigawa ba’a barta a baya ba, wajen inganta Kwalejin ta fannoni da dama tare da daukar karin sabbin kwararrun malamai don inganta sha’anin koyo da koyarwa,kana yaja hankalin dalibai wajen ganin sun himmatu don kara daukaka kwalejin da jihar Jigawa dama kasa baki daya.
@Kabir Getso