NITDA Ta Yi Gargadi Game Da satar Bayanai Da Manhajojin Kiwon Lafiya Ke Yi

Mr Kashifu Inuwa Director General National Information Technology Development Agency NITDA
Mr Kashifu Inuwa Director General National Information Technology Development Agency NITDA

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta NITDA, ta yi gargadi game da karuwar barazanar kutsen bayanai ta manhajojin wayar salula da ake saukewa, musammam manhajojin kiwon lafiya.

Shugabar sashen hulda da jama’a ta hukumar, Hadiza Umar ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja.

A cewarta, an gano matsalar ta kutsen bayanan ne cikin wani binciken da ya nuna cewa, adadi mai yawa na manhajojin kiwon lafiya na karfafa satar bayanai, wanda ke katsalandan ga sirrin jama’a.

Karanta Wannan: Kere-Keren Kayan Aikin Gona Ne Mafita Ga Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Nan-Parfesa Zilkifili Abdu.

“Manhajojin kiwon lafiya da galibinsu ke kan dandalin Android da ake saukesu daga manhajar Google Play Store, na jigilar bayanai ta hanyoyi marasa aminci”

“Wadannan bayanai da manhajojin ke tattarawa, na barazana ga tsaron masu amfani da su, domin ba samun bayanan kadai manhajojin ke yi ba, har ma da rarrabasu ga wasu kafofi”

“NITDA na kira ga jama’a su daina sauke manhaja daga wasu kafofi na daban, domin kaucewa barazanar tsaro da na kutsen bayanansu yayin da suke amfani da wayar salula”

Ta kuma bukaci jama’a su rika karanta tanadin neman izini na manhajoji kafin da bayan saukesu, domin kare bayanasu.

Karanta Wannan: Gwamnatin jihar Kano ta hada kauyuka 5 da turakun lantarki na kasa

Ta kuma shawarci jama’a su tuntubi sashen tunkarar batutuwan da suka shafi Kumfyuta na hukumar wato (CERRT) ta wannan adireshi- cerrt@nitda.gov.ng; ko kuma support@cerrt.ng; ko lambar waya – 08178774580, domin neman karin bayani. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here