Gwamnatin jihar Kano ta hada kauyuka 5 da turakun lantarki na kasa

power station new 2
power station new 2

Gwamnatin jihar Kano, ta hada kauyuka 5 na yankin karamar hukumar Minjibir ta jihar, da turakun lantarki na kasa.

Kwamishinan raya yankunan karkara na jihar, Musa Iliyasu kwankwaso ne ya bayyana hakan.

Musa Iliyasu Kwankwaso, wanda ya kaddamar da ayyukan ya ce manufarsu ita ce, inganta zamantakewa da tattalin arzikin mazauna yankunan karkara.

Wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar, Lawan Hamisu Dan Hassan ya fitar ga manema labarai, ta ce kauyukan 5 sun hada da Audaran da Gidan Dali da Gidan Tata da Gidan Makera da kuma Gidan Yanhula.
Har ila yau, Kwamshinan ya kuma duba aikin kafa sabuwar transifoma mai karfin Kva500 a yankin Zawaciki na karamar hukumar Kumbutso, wanda za a kammala cikin mako guda.

A cewarsa, wannan zai samar da karin damarmakin ayyukan yi ga mutanen yankin da ma wadanda ke kewaye da su.

Ya kuma bukace mazaunan da sauran al’ummar jihar, da su kare kayayyakin gwamnati, tare da kai rahoton duk wani yunkurin da ba su aminta da shi ba.

Da farko, manajan daraktan hukumar kula da samar da lantrki a yankunan karkara Garba Uba-Muhammad, ya yabawa gwamnatin jihar bisa kokarinta na inganta yankunan karkara da mazaunansu, ta hanyar samar da ababen more rayuwa da suke bukata.

Shi ma Kansila mai wakiltar unguwar Kwalkiya ta karamar hukumar Minjibir, Musa Hussain da shugaban yankin Zawaciki, Kamilu Aminu Kura, sun yabawa gwamnatin jihar, tare da alkawarin tabbatar da kare kayayyakin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here