Tinubu zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya yau da karfe 7 na dare.

Bola Tinubu sabo sabo.jpeg

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasa a wani shiri da za a watsa a yau.

Dele Alake, mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan ayyuka na musamman, sadarwa, da dabaru ne ya bayyana hakan.

A cewarsa, za a watsa shirin da karfe 7 na yamma ranar Litinin, 31 ga Yuli, 2023.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasar a ranar Litinin, 31 ga Yuli, 2023 da karfe 7 na yamma.”

Sanarwar ta ce, “An umurci gidajen talabijin, gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su hada kai da ayyukan sadarwar Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya da Rediyon Najeriya domin yada shirin.

Tinubu ya yi alfahari, ya ce cire tallafin man fetur da sauran manufofinsa sun riga sun haifar da sakamako yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan matsalar tattalin arziki.

Ba a dai san ko ina jawabin zasu fuskanta ba amma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da talakawa ke korafin halin kuncin da kasar ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur, lamarin da ya janyo tashin farashin man fetur.

Shugaban ya sha yin kira da a kwantar da hankula, yana mai cewa gwamnatinsa na aiki tukuru don ganin ‘yan Najeriya sun zauna lafiya.

Jawabin nasa na zuwa ne a jajibirin zanga-zangar da kungiyoyin kwadago suke yi a fadin kasar, kuma a cikin yajin aikin kungiyar likitocin Najeriya NARD wadda ta yi watsi da karin kashi 25% na albashin ma’aikata da gwamnatin tarayya ta sanar a kwanakin baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here