Gwamnatin Kano ta ce dalilin sanya hotun sarkin Kano na goma 14 Malam Muhammadu Sanusi a dakin taro na Coronation, shine saboda an gina gurin ne domin nadin shi da za’ai a matsayin sarkin Kano bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero a shekarar 2014.
Hakan na kunshe cikin jawabin da sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yiwa jaridar Solacebase rananr Litinin.
Sunusi Bature ya ce a ka’ida hotun sarki sunusi ba za’a taba cire shi daga dakin taro na Coronation ba har abada saboda tarihi.
Ya kuma kara da cewa yanzu haka ana gyaran dakin taro ne domin kawatashi da kum dawo da kimar sa.
Jaridar solacebase ta rawaito cewa tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya cire Malam Muhammadu Sanusi II daga karagar mulkin sa a watan Maris na shekarar 2020, bisa zargin sa da yiwa gwamnatin sa zagon kasa.













































