Alkalin babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja, Peter Mallong, ya rasu.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ruwaito cewa Alkalin ya mutu ne ranar Lahadi a Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.
A wani bangaren magatagar dar kotun,
Hassan Amida Sulaiman, shima ya tabbatar da rasuwar tasa a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Litinin da safe.












































