Shugaban kungiyar Malaman Jami’o’i Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa kungiyar na shirin kawo karshen yajin aikin da ta kwashe watanni bakwai tana yi.
Osodeke ya ce za a iya cimma hakan ne kawai idan an cimma matsaya ta zahiri da gwamnatin tarayya.
Osodeke ya bayar da wannan tabbaci ne a Abuja lokacin wani taro na kasa da kasa kan ilimin manyan makarantu.
Idan za a tunawa kungiyar ASUU ta fara yajin aikiin ne tun a ranar 14 ga Fabrairu wanda hakan ya sa ta shafe watanni bakwai da rufe jami’o’in gwamnati a fadin kasar nan.
A kwanakin baya ne dai gwamnatin tarayya ta maka kungiyar ASUU kara a kotun da nufin kawo karshen yajin aikin.
“Bisa dukkan alamu wadannan batutuwa mun bai wa gwamnati mafi karancin abin da za mu iya karba, amma ba su ce mana komai ba kan batun sake farfado da su, da batun alawus-alawus da aka samu da kuma batutuwan da muka tattauna.
” Mun yi shawarwari kuma mun amince su sanya hannu kuma wannan abu ne mai sauki da za a iya yinsa cikin kankanen lokaci da bai fiye kwana daya ba.
” Akan batun tsarin biyan albashi UTAS da IPPIS, sai mukace a bamu daftari muyi nazari, mu duba wanda yafi dacewa da mu, mu dauka kamar yadda muka amince.
Akan haka Osodeke ya nanata kudurin kungiyar na komawa makaranta idan gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan kudirin bayan tattaunawar.
Shugaban ASUU ya bayyana bacin ran sa kan karar da gwamnati ta kai kungiyar kotu.
Ya ce shigar da kungiyar kara gaban kotu abu ne da zai kara dagula al’amuran dalibai da manyan makarantun kasar nan.
Don haka ya yi kira ga iyaye da dalibai da su yi kira ga gwamnati da ta yi abin da ya kamata domin yajin aikin ya zo karshe ba tare da cutar da kowanne bangare ba.
Wata me fafutukar cigaban ilimi Uwargida Vivian ta ce ya kamata bangarorin biyu su kawo karshen rikicin don kare hakkin dalibai da kuma ci gaban ilimi a kasar nan.
Kungiyar ASUU ta ce wasu daga cikin batutuwan da suka haifar da yajin aikin da kungiyoyin keyi sun hada da rashin sakin asusun farfado da tattalin arziki, rashin biyan alawus alawus dakuma sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009.










































